DuniyaLabaran KasaTsaro

Najeriya da Faransa za suyi aiki tare don yakar matsalar tsaro

Shugaban kasa Muhammadu Buhari da takwaransa na Faransa Emmanuel Macron sun amince za suyi aiki tare, don kawo sabbin dabarun da za su yaki matsalar rashin tsaro dake addabar yakin tabkin Chadi dama sauran sassan kasashen Sahel.

Babban mai taimakawa shugaban kasa Buhari kan kafafen yada labarai Malam Garba Shehu ne ya shaida hakan cikin wata sanarwa da ya fitar.

Cikin sanarwar Malam Garba Shehu na cewa shugabannin biyu sun cimma matsayar ne a wani zama da suka yi a birnin Paris na kasar ta Faransa.

Macron dake zaman mai masaukin shugaba Buhari a taron da yake halarta a kasar, ya bayyana goyon bayansa ga Najeriya wajen fuskantar matsalolin tsaro.

A yayin taron da shugaba Buhari ke bayyana matsalolin da kasar nan ke fuskanta da kasashen dake makwabtaka da ita, ya kuma bayyana matakan da Gwamnatinsa ta dauka wajen magance matsalolin ciki kuwa har nada sabbin shugabannin tsaro.

Shugaban kuma ya bayyana aniyarsa na yin aiki tare da kasar Faransa da sauran kawayenta don dawo da cikakken zaman lafiya a Najeriya.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button