Labaran Kasa

Nan da Shekara 2 dole ayabawa Shugaba  Buhari>>Femi Adesina

Fadar Shugaban kasa ta bayyana cewa, nan da shekaru 2 duk kiyayyar makiyi sai ya yabawa shugaban kasa Muhammad Buhari.

Wannan na kunshene a cikin sakon cika shekaru 6 da shugaba Buhari yayi akan mulki da fadar Shugaban kasar ta fitar ta hannun kakakinsa, Femi Adesina.

A ranar 29 ga watan Mayu ne, Shugaban kasa, Muhammadu Buhari ke cika shekaru 6 akan karagar mulki.

Adesina ya bayyana cewa, gwamnatin Shugaban kasar ta samu nasara sosai a bangarori da dama. Inda yace amma akwai masu cewa basu ga komai ba.

Yace amma nan da shekaru 2 masu zuwa idan shugaban kasar ya zubo ayyukan raya kasa, ko da makiyansa sai sun yaba masa sosai.

 

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button