Labaran KasaTafiya

.

Kungiyar ISWAP data balle daga Boko Haram sun kaiwa Sojoji hari a wani sansanin sojojin dake Borno.

Lamarin ya farune a kauyen kwamdi dake Damboa a ranar Talata.

ISWAP din sun kona motar yaki daya da kuma wasu karin motoci 4, kamar yanda wani jami’in JTF ya bayyana. Hakanan wata majiyar tsaro ta tabbatarwa da Daily Trust harin.

Hakanan majiyar tace amma ba’a kashe soja ko daya ba, tace dalilin da yasa Sojojin suka kasa yakar Boko Haram din saboda guguwa me cike da yashi da ta taso a yankin.

Hakan na zuwane yayin da Shugaba Buhari ke shirin kai ziyara jihar Borno a ranar Alhamis.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button