Labaran KasaTsaro

Harin Yan’bindiga yayi sanadiyar Mutuwar Jami’an tsaro 5 a Zamfara

Hukumar ‘yansandan jihar Zamfara ta bayyana cewa, ‘yan Bindiga sun kashe jami’n tsaro 5 wanda suka hada da ‘yansanda 4 da jami’in hukumar NSCDC 1.

Kakakin ‘yansandan jihar, Shehu Muhammad ya bayyana haka inda yace lamarin ya faru a garin Gora na karamar hukumar Maradun.

Yace an jikkata mutum daya, ya kara da cewa lamarin ya biyo bayan artabu tsakanin jami’n tsaron da ‘yan Bindigar da suka tare hanyar Bakura zuwa Gusau.

Yace an aika jami’an tsaro kuma sun kwato bindigu 6 na jami’an tsaron da ‘yan Bindigar suka tafi dasu bayan gumurzu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button