AbinciBincikeLafiya

BINCIKE;Kwakwa tana Maganin Cutar Jeji

Manja ta samo asali ne daga bishiyar kwakwa wato “ palm trees “.

tana Kunshe da sinadarai kamar haka :

– carotene

– antioxidants

– vitamin E.

Kwakwa dai kamar yadda aka sani wata diyar itace ce mai matukar amfani ga rayuwar Dan adam, kamar yadda masana a fannin kiwon lafiya suka bayyana. Kwakwa na daya daga cikin ‘ya’yan itace mai matukar amfani, saboda da irin sinadarin da Allah Ubangiji ya tanadar a cikin ta.

Kwakwa na dauke da ruwa cikin ta kuma har ila yau jikinta akwai tsoka wanda akan iya barewa sannan  a ci. Kwakwa ta rabu kashi biyu, akwai kwakwar manja hakanan kuma da akwai kwakwa wace bata dauke da manja.

Dukkanin nau’oin kwakwa dai na dauke da sinadarai da suke da matukar amfani ga rayuwar bil’adama kamar yadda masana suka bayyana.

WANNAN SINADARAI NA MANJA SUNA INGANTA LAFIYA TA HANYOYI  KAMAR HAKA :

1)Ciwon daji

2) Cututtukan kwakwalwa

3) Cututtukan idanu

4) Cutar hawan jini

5) Cututtukan zuciya

6) Zazzabin cizon sauro

7) Rage taiba da nauyin jiki

Har ila yau masana a fannin kiwon lafiya sun bayyana kwakwa da cewa tana kara lafiya da walwallan jiki ga bil’adama.

Saboda sinadarin “insulin” dake cikin kwakwa, masana sun bayyana cewa, kwakwa ana rage barazanar kamuwa ko radadin cutar kansa (cancer) a jikin bil’adama.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button