Tsaro

An kama matasa su hudu da zargin satar awaki a Kano

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kano ta cafke wasu mutane hudu da ake zargi da satar awaki a yankin unguwar Sani Mainagge da ke jihar.

Kakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, wanda ya bayyana hakan  cikin wata sanarwa a ranar Talata, 25 ga watan Mayu, ya ce matasan da ake zargin sun kware a harkar satar dabbobi.

An kama sune bayan da wani matashi ya gansu a cikin babur mai kafa uku tare awaki ya kai rahoton ga hukumar yan sanda.

Yace, samun rahoton keda wuya nan take tawagar Operation Puff Adder suka garzaya zuwa gurin,amma lokacin da suka hangi ’yan sanda, sai wadanda ake zargin suka tsere.

 

Amma daga baya anyi nasarar kame hudu (4) daga cikin wadanda ake zargi, wadanda suka hada

da Aminu Musa, dan shekaru 18, Sani Abdullahi, dan shekaru 18, Huzaifa Jafar, mai shekaru 18 da Rabiu Lukman, mai shekaru 17, duk a wurin Sani Mainagge, jihar Kano.

Abubuwan da aka kwato daga wadanda ake zargin sun hada babur mai kafa uku, akuyoyi biyu amma anyaka daya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button