Da dumi-dumiLabaran Kasa

Zamu rufe duk wani Shafin sada Zumunta da zai kawo rabuwar Kaiba

Gwamnatin tarayya tace zeta kulle duk wani shafin sada zumunta dake bari ana amfani dashi wajan yada bayanan rarrabuwar kan ‘yan Najeriya.

Ministan yada labarai da Al’adu, Alhaji Lai Muhammad ne ya bayyana haka a gaban kwamitin kula da labarai da Shari’a na majalisar tarayya.

Yace Twitter sai ta yi rijista a Najeriya a matsayin kamfani kamin a yadda da ita, yace suna amfana da Najeriya amma kuma ofishin kamfanin yana kasar Ghana. Yace dakatar da Twitter ba tauye hakkin  fadar Albarkacin baki bane, saboda suna bari ana amfani dasu wajan kawo rarrabuwar kawuna.

Ya kara da cewa, ba zasu yi wata-wata ba waja kulle shafukan Instagram,  WhatsApp,  da Facebook idan aka samesu suna bari ana watsa abin da zai kawo rarrabuwar kawuna a Najeriya.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button