Da dumi-dumiLabaran Kasa

Rundunar Yan sandan Jihar Legas tayi shelar Cafke masu laifi 1,320.

Rundunar ‘yan sanda a jihar Legas ta ce ta cafke mutane wadanda ake zargi da aikata laifuka daban-daban su 1,320 kuma ta kwato makamai 110 tsakanin 1 ga Mayu zuwa 13 ga Yuli.

Kwamishinan ‘yan sanda a jihar Legas, CP Hakeem Odumosu, ne ya bayyana hakan  yayin da yake ganawa da manema labarai a Legas ranar Laraba.

Odumosu ya ce an kwato harsasai guda 125 da motoci takwas da aka sace.

Odumosu, wanda ya danganta kamun da kafa wasu rundunoni na baya-bayan nan, ya kara da cewa rundunar ta kuma iya dakile kararraki 46 na fashi da makami a cikin wannan lokaci.

Ina so in sake jaddada aniyarmu da jajircewarmu na yin amfani da duk wata hanya ta rage aikata laifuka da munanan halaye a cikin Legas, ”inji shi.

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, a ranar Laraba, ya kaddamar da sabbin sakatarorin din-din-din guda biyar a fadar shugaban kasa da ke Abuja.

Wadanda aka rantsar sune Ibrahim Yusuf (Katsina), Olusesan Adebiyi (Ekiti), Maryanne Onwudiwe (Enugu), Marcus Ogunbiyi (Lagos), da Ibrahim Abubakar Kana (Nasarawa).

An rantsar da sakatarorin dindindin jim kadan kafin fara taron mako-mako na Majalisar Zartarwa ta Tarayya.

Taron, wanda shugaban kasar ya jagoranta, ya samu halartar Mataimakin Shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo, Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha da Shugaban Ma’aikata na Shugaban Kasa, Ibrahim Gambari.

Ministocin sun kasance a zahiri yayin taron yayin da sauran mambobin majalisar suka shiga ta yanar gizo daga ofisoshin su.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button