Da dumi-dumiLabaran Kasa

Daga Karshe dai Gwamnatin Birtania tayi Magana akan kamun Nmandi Kanu.

Jakadan kasar birtaniya yayi bayani kan  raderadin da ake na cewa Shugaban haramtaciyar kungiyar BIAFRA Mazi Nmandi Kanu, an cafke shine a Kasar ta Birtaniya.                                                                                                                      A ranar Talata nan, Dean Hurlock Mai magana da yawun Shugaban ya bayyana cewa, Kanu ba a kasar Birtaniya aka kama shi ba kuma babu taimakon kasar wajen mika shi ga hukumomin kasar najeriya.   ”Zamu iya tabbatar da cewa Nmdi Kanu ba a kasar birtaniya aka damke shi ba sannan babu taimakon hukumomin birtaniya wajen mika shi zuwa Najeriya”.

Kamar yanda babban jojin Najeriya, Abubakar Malami ya bayyana ranar Talata cewa,ansami nasarar damke Nmandi Kanu ne a ranar Lahadin da ta gabata.

Ya bayyana cewa, ankama nmandi kanu ne tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na musamman.

Nmandi Kanu ya kasance mai shaidar zama dan kasa biyu wato, Najeriya da Burtaniya da ake raderadin an kamashi, inda ake tunanin yana zaune tun bayan tserewarsa daga Najeriya a shekarar 2017.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button