Da dumi-dumiLabaran Kasa

Dakarun Sojin Najeriya Sun dakile yunkurin harin Bokoharam

Dakarun soja na Operation Hadin Kai, da aka girke akan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu, sun ceto mutane 17 daga hannun ‘yan ta’addan Boko Haram a cikin Borno.

Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Birgediya-Janar. Onyema Nwachukwu, ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa a ranar Talata a Abuja.

Ya ce ‘yan ta’addar sun yi yunkurin kutsawa cikin kauyen na Auno ta hanyar layin dogo da ke makwabtaka da yankin amma kuma nan da nan sojoji suka tare su.

A cewarsa, ci gaba da yin Amman da sojojin na 7 Division Garrison da bataliya 212, ya sa aka samu nasarar kubutar da fararen hular da ke kan hanyar, wadanda aka sace a yayin harin a Kontori da ke kan hanyar Maiduguri zuwa Damaturu.

Ya ce, fararen hular da aka kubutar an yi musu cikakken bayanai tare da mika su ga jami’an rundunar da ke hanzarta daukar mataki.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button