Labaran KasaYanzu-yanzu

Gawar Marigayi Attahiru ta isa birnin tarayya Abuja

Matar marigayi Janar Attahiru ta isa wurin Sallar Jana’izar mijinta

Matar marigayi Janar Attahiru ta isa wurin Sallar Jana’izar mijinta a Masallacin birnin tarayya Abuja.

Matar Babban hafsan sojan kasar nan Janar Attahiru ta isa Babban Masallacin Abuja domin sallar Jana’izar mijinta da Allah yayi wa rasuwa sakamakon hatsarin jirgin sama a jiya Juma’a.

Tuni gawar marigayi Laftanar Janar Ibrahim Attahiru da sauran manyan sojoji 10 da suka mutu a hatsarin jirgin saman jiya Juma’a suka isa birnin tarayya Abuja, ta filin jirgin saman Nnamdi Azikwe.

Jirgin sojan saman kasar nan mai lamba C-130 ne ya dauko gawarwakin a yau da misalin karfe 10:50 na safiyar yau Asabar.

Sai dai manema labarai basu samu sukunin daukar hotuna ba, dai-dai lokacin da ake fito da gawarwakin daga cikin mota.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button