Da dumi-dumiLabaran Kasa

Gwamnatin Jihar Kebbi ta Amince da biyan Albashin Watan Yuli

""

Gwamnan Jihar Kebbi, Sanata Abubakar Atiku Bagudu, ya amince da biyan dukkan albashin watan Yuli ga daukacin ma’aikatan jihar.

A wata sanarwa da aka rabawa manema labarai ta hannun mai ba gwamna shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Yahaya Sarki, ya nuna cewa Kwamishinan Kudi, Ibrahim Muhammed Augie ne ya sanar da amincewar a ranar Alhamis.

Augie a cikin sanarwar ya nuna cewa wannan abin da gwamnan ya yi shi ne bai wa ma’aikatan gwamnati damar gudanar da Idin el-Kabir cikin annashuwa tare da danginsu.

“Mai Girma, Gwamna ya aminta da biyan albashin a duk fadin jihar da Kananan Hukumomi a yau 15 ga Yuli, 2021.

“Tuni, Ma’aikatar Kudi ta kammala shirye-shirye don daga yanzu ta biya dukkan albashi wata hanyar Bankin Tsara Kasa na Najeriya don kaucewa jinkirin da ake samu wajen amfani da bankunan kasuwanci.

“Kowane ma’aikaci za a ba shi kudaden shi nan da nan da na sako su. Mai Martaba yana yi wa dukkan ma’aikata fatan barka da Idi ”, in ji shi.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button