Labaran KasaTsaro

Hotuna: Makwabta sun sace dan makwabci sun nemi abiya fansa a zariya

Yansanda a jihar Kaduna sun tabbatar da kamun wasu matasa 3 da suka hada baki dan sace dan makwabta a Tudun Jukun dake Zaria.

Kakakin ‘yansandan Jihar, Muhammad Jalige ya bayyanawa manema labarai cewa, mutumin me suna Malam Sama’ila ya kai karar cewa an sace masa Da wanda bai san inda aka kaishi ba.

Yace wanda suka sace yaron sun kira mahaifin inda suka nemi ya kai musu Miliyan 1,500,000 indai yana son ganin dansa. Da aka ci gaba da tirka-tirka dai, sun amince akan Naira Dubu 50.

Bayan an saki yaron, ya rika kiran sunan wani Sani Sa’adu wanda makwabcinsu ne, hakan yasa aka kaiwa ‘yansanda Rahoto inda suka kamashi suka fara bincike, kuma ashe shine babban wanda ya jagoranci ta’asar.

Akwai kuma Abdullahi Usman da Usman Idris da yace tare suka yi aika-aikar. Yace duka an kamasu kuma suna fuskantar bincike wanda daga baya za’a gurfanar dasu a gaban Kotu.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button