Labaran Kasa

JAMB; Babu Maganar Sake Jarabawa ga Wadanda suka Fadi

Hukumar shirya jarrabawar share fagen shiga jami’a ta Najeriya wato JAMB, ta musanta wani labari da ke yawo a shafukan sada zumunta a kasar da ke cewa za a sake gudanar da jarrabawar ta wannan shekara.

Wani hoto da ake yadawa a shafukan ya nuna wata sanarwa da ake cewa hukumar ce ta wallafa a shafinta na twitter, inda sanarwar ke cewa za a ba wa dalibai damar sake zana jarrabawar ta wannan shekara saboda yadda yawancinsu suka fadi wanwar.

Mai magana da yawun hukumar ta JAMB Fabian Benjamin ya shaida wa BBC cewa yanzu haka hukumar ba ma ta amfani da shafin twitter tunda gwamnatin ƙasar ta hana, ballantana a ce daga wurinta sanarwar ta fito.

Wasu rahotanni dai na cewa daliban da suka zana jarrabawar ta JAMB a bana da dama sun fadi, sai dai har yanzu hukumar bata fitar da alƙaluman wadanda suka samu nasara a hukumance ba.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button