Da dumi-dumiLabaran Kasa

Jami’an Hisbah sun Cafke wata Mata mai Safarar Barasa a Jigawa

Hukumar Hisba a jihar Jigawa ta cafke wata mata mai shekaru 45 bisa zargin fasa kwauri da sayar da giya a karamar hukumar Ringim ta jihar.

Kwamanda Janar na jihar, Ibrahim Dahiru Garki ya tabbatar da kamun ga manema labarai a Dutse.

Ya ce jami’an rundunar sun kama matar ne a Ringim bayan sun samu rahoton tsaro daga mutanen kirki na yankin.

Garki ya bayyana cewa matar ta yi shigar burtu ne a matsayin matafiya, ta hanyar amfani da jakar tafiya domin shirya barasar ta kai wa kwastomomin ta.

Ya ce rundunar ta samu nasarar cafke wadda ake zargin da kwalabe casa’in da bakwai na giya iri-iri.

Kwamandan na Hisba ya ce an mika matar ga ‘yan sanda don ci gaba da bincike kafin a kai ta kotu saboda karya dokar da aka tanada.

Ya lura cewa an hana shan ko sayar da giya a jihar ta Jigawa a karkashin dokar musulunci da ta jihar.

Garki ya bukaci mutanen kirki na jihar da su sanar da rundunar a kowane lokaci da bayanai masu amfani na duk wani wuri da aikata hakan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button