Da dumi-dumiLabaran Kasa

Jami’an Yan sanda a Katsina sun kashe Yan’ bindiga 5, sun kame wasu 16 .

 

Yan sanda a jihar Katsina sun kashe mutane biyar da ake zargin’ yan bindinga ne, sun kama wasu 16 kuma sun kwato shanu 69 da miyagun kwayoyi daga hannunsu.

Kakakin rundunar ‘yan sandan  jihar, Gambo Isah, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa a ranar Laraba a Katsina.

Isah ya ce an kashe ‘yan fashin guda biyar lokacin da’ yan sanda suka yi artabu da su a Kafur, Danja, Dutsinma, Safana, Batsari da Makera a Funtua.

Ya ce an kame wasu 15 yayin artabun, yayin da, Musa Shamsudin, 25, an kame shi bisa zargin shiga daji don yi wa yan bindinga da basu da lafiya da wadanda suka samu raunuka magani.

A cewar Mista Isah, an kwato bindigogi kirar Ak47 guda uku tare da harsasai katon 10 da kuma guntayen da aka kera a wurin daga hannun ‘yan bindigan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button