Labaran Kasa

Jami’an Yan’Sanda sun ceto daya daga Cikin Daliban Makarantar Betel

Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Kaduna ta ce jami’anta da jami’an Civilian-JTF, sun kubutar da daya daga cikin dalibai 121 da aka sace daga makarantar Baptist High School, Maraban Rido da ke karamar hukumar Chikun ta Jihar Kaduna a makon da ya gabata.

Rundunar ta ce an samu nasarar kubutar da wasu mutum biyu da aka yi garkuwa da su.

A cewar jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda (PPRO), ASP Mohammed Jalige, a cikin wata sanarwa, an yi garkuwa da sauran mutanen biyu da aka ceto kwanan nan a kan hanyar Kaduna zuwa Kachia.

Rundunar ta ce an kubutar da mutanen uku a yayin aikin sintiri da aka saba gudanarwa a dajin kauyen Tsohon Gaya na karamar hukumar Chikun.

“An kwashe wadanda lamarin ya rutsa da su kuma an garzaya da su zuwa asibitin‘ yan sanda da ke Kaduna a yanzu haka ana kan sake farfado da su sannan daga baya za a mika su ga danginsu.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button