Da dumi-dumiKasuwanci

Kamfanin kwashe Shara na CAPEGATE zai sarrafa Shara izuwa Wutar Lantarki

Kamfanin kwashe shara na CAPEGATE ya kudiri aniyar samar da wutar lantarki da iskar Gas da kuma takin zamani nan da shekaru biyar masu zuwa.

Shugaban sashen gudanawar na kamfanin Bello Abba Yakasai ne ya bayyana hakan  yayin zanatawar sa da gidan jaridar dailynews24 a yau Talata .

kamfanin wanda a kwanakin baya ya kulla yarjejeniyar kwantagari da Gwamnatin Kano na tsawon shekaru ashirin da niyyar kawar da gurbatar yanayi tare da tsaftace jihar kano ta hanyar kawar da  shara daga kasuwanni da unguwanni da kuma dagwalaon masana’antu domin sarrafata zuwa wutar lantarki a fadin jihar.

Yakasai yace,nan da wani lokaci shara zata kasance kan gaba wajen samar da wutar lantarki , kamfanin zai samar da 150WT na wutar lantarki nan da zuwa shekaru biyar.

Yace, kamfanin zai samar da ayyukan yi 4500 ga matasa wadanda suka kammala karatu, ya kuma kara da cewa kamfanin cikakkaen dan kasane wanda kashi 90 na ma’aikatansa yan kasar nan ne.

Yayi kira kuma ga mutanen kano dasu kasance masu tsaftace muhalli domin kaucewa cututtuka da matsalolin yau da kullum , ya bada misali da kasashe irin su UAE wanda adacen basukai kasar nan ba amma yanzu suni fuce .

Daga karshe ya bukaci hukumomin kasashen ketare dasu sa hannu domin inganta aiyukan kamfanin kuma yayi kira ga al’umar kano dasu marawa shirin baya.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button