Duniya

Libya ta Bude Babbar Hanyar da ta hade Gabashi da Yammacin Kasar

Aikin bude hanyar da ta hade gabashi da yammacin Libya.

Gwamnatin Libiya ta bude babbar hanyar da ta hada yankunan gabashi da kuma yammacin kasar da suka jima a rabe, sakamakon yakin basasar da yayi sanadiyar  kifar da gwamnatin tsohon shugaban kasar Mu’ammar Gaddafi a shekarar 2011.

Fira Ministan Libya Abdul Hamid Dbeibah ya jagoranci kawar da guma-guman duwatsu da kuma tarin kasar da aka yi amfani da su wajen raba yankunan na Yammaci da Gabashin Libya.

An dai shafe tsawon lokaci ana fafatawa tsakanin Sojojin Gwamnatin Libya da mayakan Janar Khalifa Haftar da ke iko da yankin gabashin kasar, kafin daga bisani a cimma yarjejeniyar sulhun da ta kai ga kafa sabuwar gwamnati a karkashin Fira Ministan Abdul Hamid.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button