Da dumi-dumiDuniya

Mafusata a Kasar Africa ta Kudu na alwashin zubar da jinin yan Najeriya

Yanzu haka a birnin Soweto na kasar Africa ta kudu, wata kungiya na  Zanga-Zangar kyamar baki ‘yan Najeriya.

Masu Zanga-Zangar sun sha Alwashin zubar da jinin ‘yan Najeriya da sauran ‘yan kasashen waje ko kuma su bar birnin, kamar yanda Sahara Reporters ta ruwaito.

Birnin Soweto shine gaba-gaba wajan fara Zanga-Zangar kyamar baki da ake fuskanta a kasar ta Africa ta Kudu.

Wani dan Najeriya, Lauya dake zaune a kasar, ya bayyana cewa, ‘yan siyasa na amfani da irin wannan dama wajan tunzura matasa dan su samu karbuwa.

Hakanan kuma, kishin kasuwancin ‘yan kasashen waje dake samun karbuwa nasa matasan kasar fara irin wannan Zanga-Zangar.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button