Duniya

Malamin ya Haramta amfani da Emoji a Shafin Sada Zumunta .

Wani fitaccen malamin addinin Islama a Bangladesh da ke da ɗimbin magoya baya a shafukan intanet ya gabatar da wata fatawa inda ya ce haramun ne yin amfani da alamar dariya (emoji) domin muzanta mutane.

Malamin mai suna Ahmadullah, da ke amfani da suna ɗaya yana da sama da mabiya miliyan uku a Facebook da YouTube, kuma yana yawan wa’azi a kafofin talabijin.

Ya wallafa wani bidiyo na tsawon minti uku a shafinsa inda ya yi bayani kan yadda ake cin mutunci da muzanta wasu a Facebook.

A cikin fatawarsa ya yi bayanin haramcin amfani da alamomi na dariya ga musulmi da ake amfani da su a shafukan sada zumunta na intanet.

Sama da mutum miliyan biyu suka kalli bidiyon inda a ciki ya ce: “A zamanin yau muna amfani da alamar Facebook ta haha emojis don zolayar mutane.”

Malamin ya ce: “Idan mun yi amfani da alamar dariya da nufin wasa daidai da niyyar wadda ya wallafa wani saƙo, to wannan ba laifi ba ne.”

“Amma idan abin da kuka yi na nufin yin izgili ko izgilanci ga mutanen da suka sanya ko yin tsokaci a shafukan sada zumunta, to haramun ne a Musulunci,” in ji shi.

Malamin kuma ya yi kiran a ƙaucewa yin amfani da alamar da nufin yin dariya ga wani. Ya ce ɓata ran musulmi har ya kai ga furta wasu  kalamai marar daɗi, babu kyau.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button