Tsaro

Matar Bola Tinubu ta soki Sanatan da ya ce babu tsaro a Najeriya

Wasu ‘yan majalisar dattawan Najeriya sun yi musayar zafafan kalamai sakamakon rashin tsaron da ke ci gaba da ta’azzara a kasar.

Sanatocin, Smart Adeyemi daga jihar Kogi da Remi Tinubu daga jihar Lagos, suna cikin wadanda suka bayar da gudunmawa yayin muhawarar da majalisar dattawan kasar ta gudanar ranar Talata.

Majalisar ta yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya zage damtse domin magance rashin tsaron da kasar ke ci gaba da fama da ita tana mai shan alwashin ganawa da shi a kan batun.

A nata bangaren, majalisar wakilan kasar ta bukaci Shugaba Buhari ya ayyana dokar ta-baci a kan matsalar tsaro.

News Room

DailyNews24 provides you with the news you can trust as it breaks around the country and beyond. Since 2019, DailyNews24 delivers compelling, and visually engaging news & trends.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button