Labaran Kasa

Mawaki Davido yayi Rashin Makusanci

Mawaki Davido yayi babban rashin abokinsa, adalilin tsayawar bugun zuciya jim kadan bayan kaishi asibiti.                                                                                                                Habeeb uthman,wanda akafi sani da suna Obama DMW sun kasance abokai tun shekara 2017.

Marigayin yakai kansa Asibti domin duba lafiyarsa jim kadan kafin a tabbatar da Mutuwarsa yau Laraba, June,30,2021.

Mawakain ya Mutune bayan awanni kadan da zuwa asibitin.

Bayan saninsu da akayi da mawaki Davido, Obama DMW ya kasance kuma wanda ya kafa Kamfanin sa na waka mai suna Obama Music Worldwide OMW ,kuma ya kasance mai shirya waka da daukar nauyi.

Mamacin dai an haifeshi a garin Lagos, kuma ya kasance a harkar waka tunkafin haduwar sa da Davido sannan daga bisani ya bude nashi kamfanin OMW.

Takwaransa Peruzzi, wanda shima mawaki ne karkashin Kamfanin DMW, ya nuna alhininsa inda yayi rubutun jimami a shafinsa na instagram “Lord have mercy”, “1 love 1 life”, “That’s a real 1 gone BTW”.

Obama yana daya daga dikin makusantan mawaki Davido, wadanda suka mutu abaya bayan nan. A watan disemba na shekarar 2020, mai tsaron lafiyar mawakin Tijjani Olamilekan aka TeeJay ya mutu bayan fama da gajeriyar rashin lafiya, hakanan kuma a shekarar 2017 mawakin yayi rashin mutum uku daga dikin abokansa dukansu a sati guda.

Za’a gudanar da zana’idar Obama kamar yanda addinin Musulunci ya tanada.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button