Labaran KasaSiyasaTsaro

Mun shirya tsaf don haduwa da Malami a kotu kan maganar Makiyaya – Akeredolu

Kungiyar Gwamnonin kudancin kasar nan ta ce tana nan kan bakarta na tabbatar da matakin haramta kiwon sake a yankunan su.

Wannan na cikin wata sanarwa da Gwamnan jihar Ondo ya fitar, dake zama martini ga maganar Ministan shari’a kan cewar matakin ya saba da kundin tsarin mulkin kasa.

Gwamnan wanda kuma shi ne shugaban kungiyar Gwamnonin kudancin kasar nan ya ce za su dauki dukkanin matakan Shari’a don ganin sun tabbatar da manufar ta su.

Cikin sanarwar kungiyar Gwamnonin kudancin ta ce babu ja da baya a wannan matakin da suka dauka.

Haka zalika sanarwar ta nanata cewa shakka babu idan Ministan ya dage, to kuwa za su shiga kotu kan manufar ta su na haka kiwon sake.

A ranar Larabar makon nan ne Ministan Shari’a ke bayyana cewa babu wani dan kasar nan da ke da ‘yancin hana wani dan kasa yawo tare da dukiyarsa, cikin wata hira da yayi da gidan talabijin na Channels.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button