Da dumi-dumiLabaran Kasa

Obasanjo da IBB sun san wanda ya Kashe Abacha da Abiola  >>FFK

Tsohon Ministan Sufurin Jiragen Sama, Femi Fani Kayode ya bayyana cewa, MKO Abiola da tsohon Shugaban kasa,  Janar Sani Abacha, CIA ne suka kashesu.

Sannan kuma yace tsaffin Shuwagabannin kasa, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da Olusegun Obasanjo sun san da maganar.

Yace an baiwa Abacha guba ne ta hannun daya daga cikin jami’an tsaron tsohon shugaban kasar Falasdinawa,  Yasser Arafat.

Ya bayyana cewa IBB da Obasanjo suma wakilan CIA ne kuma sun san da wannan shiri. Yace koda bamu san Abacha da MKO, amma abinda aka musu bai cancanta ba.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button