Labaran KasaYanzu-yanzu

Sallar Jana’iza ta manyan sojojin kasar nan

An yi wa babban hafsan soji da sauran sojoji da suka rasu Sallar jana’iza a babban masallacin Juma’a na birnin tarayya Abuja a ranar Asabar.

Hakan na zuwa ne bayan Sallar Azahar da tsakar ranar yau Asabar.

Manyan sojojin sun rasu ne sakamakon hatsarin jirgin sama a jiya Juma’a.

Rahotanni na nuni da cewa manyan jami’an Gwamnati da suka halarci jana’izar sun hada da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan da babban Sufeton ƴan sandan kasar nan Usman Alkali Baba, sai kuma ministan sadarwa Dr. Isa Pantami da sauran manyan jami’an Gwamnati.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button