DuniyaYanzu-yanzu

Saudiyya ta amince ‘yan kasashen waje su halarci aikin Hajjin bana

Kasar Saudiyya ta sahale maniyyata su je aikin Hajjin bana daga fadin duniya tare da sharadin bin dukkan matakan dakile yaduwar cutar COVID-19.

Jaridar Al-Watan ta kasar ta ruwaito wannan matakin na zuwa ne bayan hukuncin da hukumar Hajji da Umra ta kasar ta yanke a ranar 9 ga watan Mayun da muke ciki

Ma’aikatar lafiya ta kasar Saudiyyan ta ce za su ci gaba da aiki tukuru don tabbatar da cewa an kiyaye lafiyar duk wanda ya je aikin Hajji.

A gefe guda kuwa ma’aikatar ta bayyana cewa za ta fitar da matakan kare lafiya da zata shimfida ga duk maniyyacin da zai halarci aikin na bana.

Rahotanni na nuni da cewa musulmi kimanin milyan 2.5 ne ke zuwa Saudiyya da niyyar aikin Hajji a kowacce shekara daga sassan duniya, lamarin da annobar COVID-19 ta sanya kasar ta rage adadin zuwa 1000 a bara.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button