Da dumi-dumiLabaran Kasa

Shirin Aiki na Gwamnatin tarayya na 774,000 na korafi da rashin biyansu hakkokinsu

Da yawa daga cikin wanda aka dauka aikin wata 3 na 774,000 na Gwamnatin tarayya sun bayyana cewa ba’a biyasu hakkokinsu ba.

An dauko mutane 1000 daga kowace karamar hukuma ta Najeriya. Akwai alkawarin biyan Alawus din Dubu 20,000 tsawon watanni 3.

Saidai Daily Trust ta ruwaito cewa, da yawa basu samu kudin ba, yayin da wasu kuma aka biyasu kudin wata daya kacal.

Wasu kuma daga ciki sun bayyana cewa, ba’a basu wajan da zasu yi aiki ba inda wasu ke kokawa cewa an cucesu wajan biya.

Saidai a bangaren hukumar dake kula da aikin, NDE ta bayyana cewa, bankuna ne ke kawo musu tsaiko wajan biyan hakkokin ma’aikatan.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button