DuniyaSiyasaTsaro

Sojojin Mali sun kame shugaban ƙasa da Firaminista

Sojoji a kasar Mali sun kame shugaban kasa da firaminista da kuma ministan tsaro na Gwamnatin rikon kwaryar kasar ranar Litinin bayan yi wa majalisar ministocin ƙasar garambawul.

Wasu majiyoyin diflomasiyya da na Gwamnati sun tabbatar wa kamfanin dillacin labarai na ‘Reuters’ cewa, ana tsare da shugaba Bah Ndaw, da Firaminista Moctar Ouane da mimnistan tsaro Souleymane Doucoure a wani sansanin soji.

An ɗora wa Ndaw da Ouane alhakin jagorantar zaɓen sabuwar Gwamnatin farar hula cikin watanni 18, sai wasu da dama a cikin Gwamnati da ƴan adawa na bayyana fargaba kan yadda sojoji suka mamaye manyan kujerun Gwamnati.

Kamen na sun a zuwa bayan sauya wasu daga cikin sojojin da suka jagoranci juyin mulki a watan Agustan bara a majalisar ministoci.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button