Da dumi-dumiLabaran Kasa

Sunyi Mata Azaba kafin Su tafi da Ita

Wasu ‘yan bindiga wadanda yawansu ya kai 10 a ranar Laraba sun yi awon gaba da matar tsohon Shugaban Karamar Hukumar Kaugama, Alh. Ahmed Yahaya Marke, a jihar Jigawa.

Aliyu Ahmad, dan uwa ga wanda aka sace, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun afka gidan tsohon shugaban karamar hukumar da ke kauyen Marke a kan babura.

Ya ce wadda aka sacen mai suna Hajiya Fatima an yi mata duka kuma an mata azaba kafin a tafi da ita misalin karfe 1:00 na safe.

Aliyu ya bayyana cewa hudu daga cikin ‘yan bindigan, dauke da muggan makamai, sun shiga gidan yayin da ragowar‘ yan bindigar su shida suka tsaya a waje don lura da lamarin.

Ya bayyana cewa ‘yan fashin sun tuntubi dangin amma ba su sanar da kudin fansar ba

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar, ASP Lawan Shisu, shi ma ya tabbatar da faruwar lamarin ga manema labarai.

Ya lura cewa ‘yan sanda suna aiki tare da sauran jami’an tsaro don gano masu garkuwar da kuma ceto wadda aka sace.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button