DuniyaLabaran KasaWasanni

Uwargida Jill Biden ta U.S zata halarci Gasar wasannin Olympic

 Uwargidan Shugaban Amurka Jill Biden zata halarci taron bude gasar wasannin olympic, wanda zai gudana a kasar Tokyo. Sanarwar tafito ne daga White House ranar Laraba.
Ankuma ce, karin bayani sai nan gaba.

 

Sanarwar ta kuma bayyana cewa, Mai gidan nata Joe Biden bazai sami halartar gasar wasannin ba, kamar yanda jaridar Washigton Post ta bayyana.

Jami’in hudda da jam’a na White House, Jen Psaki yace Biden yana goyon bayan gasanr da zata gudan a tokyo sannan abada kariya domin kaucewa yaduwar Cutar Corona.

Bayanin tafiyar uwargidan zuwa tokyo sun fito ne kwanaki kadan bayan da hukumomin wasan suka bayyana cewa gasar zata gudana ne ba tare da yan kallo ba,sakamakon yaduwar cutar Corona dama wasu cututtukan makamantan ta.

Kasar ta Tokyo dama makwabtan ta suna a mataki na hudune a mizanin yaduwar.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button