Da dumi-dumiLabaran Kasa

An Gurfanar da Mutumin da ya shiga Coci yin Sata a gaban Kotu.

                                                                                                                                                                             Adeosun wanda ba abada cikakken bayanin sa ba ya kasance ana tuhumarsa da bannata wasu kayan Cocin.

Mai gabatar da kara, Insp E.O.Adaraloye ya fadawa Kotun cewa mai laifin dai ya aikata laifin ne a ranar 9 ga watan Juli kimanin karfe 11.30 na dare a anguwar Nice estate dake Ota.

Adaraloye ya kara da cewa, mai laifin ya balle Kyauren windon cocin wanda kudin sa yakai kimanin 3,000 mallalkin Cocin Praist Baptist Church domin yin sata.

Ya kuma ce, tuni dai wanda ake tuhuma ya amsa lifin sa

Mai sharia A.O.Adeyemi ta bada belinsa bisa kudi N20,000 da kuma wanda zasu tsaya masa tare da cinsa tara.

Sannan ta kara da cewa, wanda zai tsaya masa dole zai kasance ya halarci zaman karar kuma loe saf ya kasance ya bayyana takardun biyan haraji ga Gwamnatin jihar Ogun .

Daga karshe dai an daga sauraron karar har sai 23 ga watan Juli.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button