Da dumi-dumiLabaran Kasa

Yan Bindiga sun kaiwa Tawagar Ganduje Hari

Yan Bindiga sunyi musayar wuta da Jami’an tsaro masu rakiyar gwamna Abdullahi Umar Ganduje.                                                                                                              Yan Bindigar sun kaiwa jami’an hari ne yayin da suke kan hayar dawowa daga jihar Zamafara inda gwamnan jihar ya sauya jam’iya daga PDP zuwa APC.

Wata majiya ta bayyana cewa, Gwamna Abdullahi Ganduje da takwaransa Mai Mala Buni na Yobe da kuma Gwamna Abubakar Badaru na Jigawa basa cikin tawagar lokacin da aka kai harin.

Ankara da cewa, jami’an yan-sanda uku daga cikin tawagar sun sami rauni.

” Dukkan Gwmnonin basa tare damu. Tuntuni sun wuce don haka mune kadai aka kaiwa harin yayin da muke kan hanyar zuwa kano.” Inji wata majiya.

Wata majiyar ta kara da cewa, motar ambulans dake cikin tawagar ta tashi daga aiki.

Ankuma kara da cewa, Gwamnonin dai tuni suna gida tun kafin afkuwar lamarin.

 

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button