Da dumi-dumiLabaran Kasa

Yan’sanda a Jihar Ondo sun sami nasarar Cafke Masu Laifi 15

Ayau Laraba Yan sanda a jihar Ondo sun bayyana cewa sun sami nasarar cafke akalla Mutum biyar da ake Zargi da aikata laifuka daban daban a fadin jihar.

Kwamishinan yansanda na jihar Mr Bolaji Salami, ya bayyana hankan yayin zantawa da manema labarai agarin Akure lokacin da yake nuni da irin ci gaba da hukumar ta samu a watan da ya gabata.

Salami, ya bayyana cewa wadanda aka Kama ana zarginsu da aikata laifuka mabanbanta kama daga fashi da makami da kuma kisan kai da kuma fyade, yace sun sami nasarar kamasu awurare daban daban a fadin jihar.

Ya kara da cewa, ansami kwace babura guda 9 da kuma bindiga da kuma babbar mota makare da siminti a hannun su.

”Yau kimanin wata guda kenan da mukayi bajekolin wasu nasarori da muka samu. Hakanan kuma gashi yau muna gabatar da wata nasarar cikin wata daya” .

Ya kara da cewa, abun babu dadi yanda masu laifi suke cin karensu babu babbaka a jihar ta Ondo ba tare da ana kamasu ba.

Kamar yanda yace,” Inaso masu laifi su sani cewa ba wai nazo Ondo bane domin jin dadin kyakkawan yanayin ta, face don inkawar da duk wani ayukan bata gari a fadin jihar”.

”Don haka sauran masu laifin da suka ki barin jihar,ina mai baku wannan sakon gargadi”.

“Babu sauran wani mai laifi da zaiso yayi taho na taho da mutanena yayin gudanar da aikin tsaro”.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button