Labaran Kasa

Yan’Sanda sun kubutar da dan Shekaru 45 da Shanu 36 daga Yan’bindiga a Katsina.

Jami’an Yan’Sanda a jihar katsina sun dakile yunkurin hari yan’bindiga a kauyen layin Minister dake karamar hukumar Malumfashin jihar katsina.

SP Gambo Isah, Kakakin hukumar yan’sandan jihar ne ya bayyana afkuwar lamarin a zantarwar sa da manema labarai yau Litinin a babban birnin jihar.

Yace ” a ranar 17/07/2021 da misalin karfe 11:02 na yamma, yan bindigan bisa babura dauke da bindigu kirar AK47 suka tare wata karamar Hanya a garin na Layin Minister inda suka sace wani Mutum dan kiminin shekaru 45, wanda ya fito daga kauyen Tafkin Jege na karamar Hukumar Kafur.”

 

”Yan’sandan karamar hukumar Kankara karkashin jagorancin DPO na Kankara suka farmasu a Unguwar Nakome dake Kauyen Yar’goje, sukayi musayar wuta inda suka kubutar da wanda aka sace. Sannan kuma ankwato bindiga kirar AK47 guda daya. Kakakin ya tabbatar da hakan.

Ya kara da cewa, har’ila yau adai  wannan rana kuma da misalin karfe 5 na yamma shin wannan DPO ya kara jagorantar jami’an Yan’sanda zuwa Kauyen Majifa dake karamar hukuka Kankara inda sukayi batakashi da barayi kuma suka kwato shanu 36 da aka sace.

”Da yawn daga cikin yan’bindigan sun tsere da raunin harbin bendiga a jikin su, amma jami’an mu na suntiri sun bazama neman su da kuma zummar zamu kamasu. Hukumar yan’sanda dai ta bukaci al’umma da suci gaba da bada hadin kai ga jami’an tsaro dama hukukomi wajen samar masu da bayana masu kyau.

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button