Labaran KasaTsaro

Za mu sake fasalin kungiyoyin ‘yan banga domin matsalar tsaro>>Tambuwal

Gwamnatin jihar Sokoto ta sake jaddada bukatar sake fasali  da kuma sake kafa kungiyoyin ‘yan banga a jihar domin ba su damar karfafa ayyukan tsaro da taimaka wa Gwamnatin Tarayya a jihar.

Wannan, a cewar Gwamna Aminu Tambuwal, ya zama dole ta fuskar tabarbarewar tsaro da ake fuskanta kwanan nan a karamar hukumar Rabah dake gabashin jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a ranar Litinin a garin Gandi, karamar hukumar Rabah, inda ‘yan bindiga suka yi arangama da wasu kungiyoyin’ yan banga, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum 21.

Gwamnan yace“Za mu sake fasali tare da sake kafa kungiyoyin’ yan banga a Jihar Sokoto. Za mu tabbatar mun samar musu da baburan hawa da kayan sadarwa domin su kasance masu sadarwa da hukumomin tsaro yadda ya kamata; kuma don su samar da bayanai na asali da kuma jagora ga hukumomin tsaro, ”

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button